?>

Sri Lanka : An Umurci Sojoji Su Bindige Masu Tarnaki Ga Tsaro

Sri Lanka : An Umurci Sojoji Su Bindige Masu Tarnaki Ga Tsaro

Ma'aikatar tsaro a Sri Lanka ta umurci sojojinta kasar da su bindige wadanda ke da hannu wajen kwasar ganima, a daidai lokacin da tashe tsahen hankula masu nasaba da rikicin siyasa a kasar ke kara kamari.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Mutane takwas ne aka rawaito sun suka mutu, kana wasu sama da 200 suka jikkata da suka hada da ‘yan sanda biyu, kana an farmawa gwamnan gine-gine ana ta kwasar ganima, tun fara rikicin mafi muni.

A halin da ake ciki dai masu bore a kasar suna neman shugaban kasar Gotabaya Raja-paksa da ya sauka daga mulki, wanda ke nufin murabus din da firaminsitan kasar ya yi bai gamsar da masu zanga zangar ba.

Firaministan kasar Mahinda Raja-paksa ya yi murabus ne bayan artabun da akayi tsakanin magoya bayansa da kuma masu zanga zangar ranar Litini.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*