?>

Siriya Ta Sake Dakile Wani Harin Isra’ila Kan Birnin Homs

Siriya Ta Sake Dakile Wani Harin Isra’ila Kan Birnin Homs

Siriya, ta sanar da dalike wani harin sama na Isra’ila kan birnin Homs dake tsakiyar kasar da cikin daren jiya Laraba.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Kafofin yada labaran kasar sun rawaito cewa, wani hari ta sama da Isra'ila ta kai ya auna wasu sassan ciboyoyi a tsakiyar kasar, inda makamman garkuwa daga hare haren sama na kasra suka maida martani.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Siriya OSDH, dake da cibiya a Biritaniya, ta ce harin ya yi sanadin mutuwar mutum hudu ciki har da fararen hula biyu.

Tunda farko dai gidan talabijin din Siriyar ya ce mutum biyu sun mutu yayin harin, sai kuma sojoji shida da suka jikkata, an kuma samu barna.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*