?>

Shugaban Afirka Ta Kudu Ya Buƙaci Haɗin Kai A Кasar Sakamakon Rikicin Da Ke Faruwa

Shugaban Afirka Ta Kudu Ya Buƙaci Haɗin Kai A Кasar Sakamakon Rikicin Da Ke Faruwa

Shugaban ƙasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya buƙaci samar da yanayi na haɗin kai a ƙasar sakamakon ranaku na tashin hankali da tarzoma da ke faruwa a ƙasar yana mai jan kunnen dangane da satar kayayyakin jama’a da ƙone-ƙone da wasu suke yi.

ABNA24 : Shugaba Ramaphosan, wanda ya ke shan suka dangane da yadda yake mu’amala da rikicin da ke faruwa a ƙasar, ya bayyana hakan ne a yau ɗin nan Lahadi yayin ziyarar da ya kai garin Soweto ɗaya daga cikin wuraren da rikicin ya fi yin ɓarna, ya ce lalle akwai gazawar da aka nuna, to sai dai a cewarsa za a iya haɗa hannu waje guda wajen duba lamarin da kuma yin abin da ya dace.

Har ila yau shugaban na Afirka ta kudu ya buƙaci samar da haɗin kai tsakanin ‘yan ƙasar sama da yadda suka kasance kafin wannan rikicin in ji shi.

Duk da cewa gwamnatin Afirka ta kudun ta sanar da mutane 12 da take zargin da hannu wajen tada tarzomar da ya zuwa yanzu aka ce ta haifar wa ƙasar da hasarar da ta kai ta Dala biliyan 1, to amma mutum guda ne kawai daga cikin sha biyun aka kama shi, lamarin da shugaban ya ke ci gaba da shan suka kan hakan.

Sama da mutane 200 ne suka rasa rayukansu sakamakon wannan rikicin wanda ya faro daga batun ɗaure tsohon shugaban ƙasar Jacob Zuma da wata kotu ta yi lamarin da daga baya ya rikiɗe ya zama tarzoma da satan kayayyakin gwamnati da na jama’a.

Rahotanni dai suna nuni da cewa mutanen Afirka ta Kudun suna cikin tsanani na rashi wanda ana ganin yana daga cikin dalilin da suka sanya zanga-zangar goyon bayan Jacob Zuma ɗin ta rikiɗe ta koma tarzoma, duk da cewa wasu suna ganin akwai son zuciya da wasu suka nuna amma lamarin bai kai ga haka ba. Wasu kuma suna zargin masu adawa da gwamnatin shugaba Ramaphosa ɗin da kitsa wutar wannan tarzomar.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*