?>

Sarkin Qatar Na Gudanar Da Wata Ziyarar Yini Guda A Kasar Iran

Sarkin Qatar Na Gudanar Da Wata Ziyarar Yini Guda A Kasar Iran

Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani ya isa birnin Tehran a wata muhimmiyar ziyarar aiki ta yini guda, domin tattaunawa da jami'an kasar Iran kan batutuwan da suka shafi kasashen biyu da na yankin da ma na kasa da kasa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Mohammad Mokhber ya tarbi Sarkin Qatar a lokacin da ya isa Tehran babban birnin kasar Iran a ranar yau Alhamis.

Daga bisani shugaban kasar Iran Ebrahim Raeisi ya tarbe shi a hukumance kafin a shiga tattaunawa.

A yayin da yake jagorantar wata babbar tawaga ta siyasa da tattalin arziki, Sheikh Tamim zai tattauna da hukumomin Iran ciki har da shugaba Raeisi.

Ziyarar ta biyo bayan wata ziyarar da shugaban na Iran ya kai birnin Doha a watan Fabrairu, inda ya gana da manyan jami'an Qatar tare da halartar taron koli na shida na kungiyar kasashe masu arzikin iskar gas (GECF).

Ziyarar Raisi ita ce ta farko da wani shugaban Iran ya kai Qatar cikin shekaru 11. A yayin ziyarar, Tehran da Doha sun rattaba hannu kan yarjeniyoyi 14 na fahimtar juna, da suka hada da fannonin sufurin jiragen sama, kasuwanci, jigilar kaya, watsa labarai, soke bukatun biza, wutar lantarki, ka'idoji, ilimi da al'adu.

Qatar dai na da kyakykyawar alaka da Iran, inda take da wani katafaren filin iskar gas na hadin gwiwa tsakaninta da Iran.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*