?>

Sama Da Masana 3000 Daga Kasahen Duniya 47 Ne Suka Bukaci A Cirewa Iran Takunkumi

Sama Da Masana 3000 Daga Kasahen Duniya 47 Ne Suka Bukaci A Cirewa Iran Takunkumi

Rahotanni sun bayanna cewa adai dai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa a birnin Vienna ta cirewa iran takunkumi kimani masana 3500 daga kasashen duniya 47 ne suka rattaba hannu kan takardar yin kira da a cire takunkumin zalunci da aka kakabawa kasar iran domin take dokokin kasa da kasa ne.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A lokacin dai jami’ai daga kasashen Faransa Birtaniya Jamus china da kuma kasar Rasha suke ganawa da wakilan kasar iran a wani zagaye na tattaunawar da ake yi na cire mata takunkumi Amurka ta fice daga yarjejeniyar JCPOA a shekara ta 2018 saboda matsin lambar Isra’ila yayin da iran take aiki da dukkan yarjejeniyar da aka cimma.

Iran ta tabbatar da cewa shirin ta na Nukiliyar na zaman lafiya ne , kuma babu wani dalili da aka gabatar da yayi hannun riga da bayanan da iran ta yi na kasancewar shirin ta na zaman lafiya ne .

Iran da Alummar ta sun fuskanci hare haren ta’addanci da Barazanar kai mata farmakin soji daga bangaren Isra’ila da Amurka wanda take dokokin majallisar dinkin duniya ne a fili.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*