?>

Sakon Jagora Na Hajji : Juriya Ce Za Ta Kawo Karshen Tsoma Bakin Amurka A Cikin Kasashen Musulmai

Sakon Jagora Na Hajji : Juriya Ce Za Ta Kawo Karshen Tsoma Bakin Amurka A Cikin Kasashen Musulmai

Jagoran juyin juya halin musulinci na Iran, Ayyatollah Sayyid Ali Khamenei, ya fitar da sakonsa na Hajji kamar yadda ya saba yi ko wacce shekara.

ABNA24 : Bayan godiya ga Allah, Ubangijin talikai, da neman tsira da aminci ga ma’aikinsa Muhammad (SAW), jagoran juyin juya halin musulinci na Iran, ya bayyana cewa wannan ita ce shekara ta biyu ta rashin jin dadi da musulmi basu samu damar gudanar da aikin hajji ba, sakamakon annobar korona, ko wata killa manufofin wadanda suka mamaye massallacin Ka’aba mai tsarki sun hana masu imani ganin al’kibilarsu.

Jagoran ya kara da cewa, Wannan jarabawar ta yi kama da sauran abubuwan da suka gabata a tarihin al'ummar musulmi, wanda zai iya haifar da kyakkyawar makoma.

Abin da ke da muhimmanci shi ne cewa ko ba’a gudanar da aikin Hajji ba, ya kasance a raye a cikin zukata da rayukan Musulmai.

Irin jawabin da Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ke fitarwa wadanda ke girgiza kasashe masu girman kai na duniya, shi ne zai iya zamo makami na kawo karshen tsoma bakin Amurka da kuma kasashe ‘yan takala.

‘’Da juriya ne kawai za’a iya kawo karshen tsoma bakin Amurka a cikin harkokin kasashen musulmai’’ inji jagoran.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*