?>

Sabon Nau’in Covid-19 Na Barazana Ga Farfado Tattalin Arzikin Amurka

Sabon Nau’in Covid-19 Na Barazana Ga Farfado Tattalin Arzikin Amurka

Amurka ta nuna damuwa a game da sabon nau’in cutar korona na Delta, da kuma sauren nau’in cutar dake iya zama babbar barazana ga yunkurin farfado da tattalin arziki.

ABNA24 : Da take sanar da hakan, sakatariyar baitalmalin Amurka, Janet Yellen, ta ce muna da damuwa sosai game da nau’in Delta na korona mai saurin yaduwa dama wasu nau’ukanta wadanda zasu iya zama barazana ga tattalin arziki.

Ta kara da cewa abunda ke faruwa a wasu sassan duniya, yanzu yana kan bazuwa a dukkan kasashen duniya.

Nau'in Delta ya yi kamari a kasashen Amurka da Birtaniya da Indonesia kuma yana cigaba da yaduwa a wasu kasashen.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*