?>

Rouhani: Iran Na Fatan Kammala Yi Wa ‘Yan Kasarta Rigakafin Corona Cikin Kankanin Lokaci

Rouhani: Iran Na Fatan Kammala Yi Wa ‘Yan Kasarta Rigakafin Corona Cikin Kankanin Lokaci

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya bayyana cewa, gwamnatin kasar na fatan ganin ta kammala yi wa ‘yan kasar rigakafin cutar corona a cikin kankanin lokaci.

ABNA24 : Shugaba Rouhainin ya bayyana hakan ne a yau Lahadi, a lokacin da yake ganawa da ma’aikatan hukumar yaki da cutar corona ta kasa a birnin Tehran, inda ya bayyana cewa, suna fatan ganin an kammala yi wa dukkanin ‘yan kasa allurar rigakafin corona a cikin kankanin lokaci.

Rouhani ya ce dukkanin bangarorin kiwon lafiya suna yin iyakacin kokarinsu domin tabbatar da cewa aikin nasu ya yi nasara wajen dakile yaduwar wannan cuta, kamar yadda ita ma a nata bangaren gwamnati, nauyi ne da ya rataya a kanta wajen samar musu da dukkanina bubuwan da suke bukata a wannan aiki.

Ya kara da cewa, nauyin yaki da yaduwar cutar corona da kuma dakile ta, ba takaitu a kan gwamnati da bangaororin kiwon lafiya ba kawai, nauyi ne da rataya a kan kowa ta fuskoki daban-daban, da hakan ya ada da kiyaye ka’idojin da aka gindaya na kiwon lafiya, da kuma daukar matakan kariya, saka takunkumi, bayar da tazara wanke hannu da sauransu.

Baya ga haka kuma shugaba Rauhani ya yi ishara da cewa, Iran tana daga cikin kasashen da suka fuskanci babban kalu bale dangane da wanann annoba, amma a cikin taimakon Allah da kuma himma ta jami’ai a bangaren kiwon lafiya, an samu nasarar rage kaifin yaduwa da kuma kamuwa da cutar, gami da irin hasarar rayuka da aka rika samu a lokutan baya.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*