?>

Rasha Ta Yi Kira Ga Kasashe Masu Arziki Su Gudanar Da Taron Tara Kudin Sake Gina Tattalin Arzikin Afganistan

Rasha Ta Yi Kira Ga Kasashe Masu Arziki Su Gudanar Da Taron Tara Kudin Sake Gina Tattalin Arzikin Afganistan

Jakadan kasar Rasha a birnin Kabul babban birnin kasar Afganistan ya yi kira ga kasashen duniya masu arziki su gudanar da taro don tara kudade wadanda za'a sake gina tattalin arzikin kasar Afganistan da su.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : yana fadar haka a yau. Ya kuma kara da cewa, yana fatan kasashen da suka lalata tattalin arzikin kasar Afganistan su ne zasu zo sahun gaba don gudanar da wannan taron. Samir Kabulov ya ce manufar taron ba wai tarwa kungiyar Taliban kudade bane sai dai tada komadar tattalin arzikin kasar Afganistan zai hana mutanen kasar ficewa daga kasar.

Har'ila yau jakadan ya soki kungiyyin agaji wadanda suka dakatarda ayyukan agaji na biliyoyin dalolin Amurka a kasar Afganistan bayan da kungiyar taliban ta kwace iko da kasar.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*