?>

Rasha Ta Yaba Da Sakamakon Tattaunawar Iran Da Hukumar IAEA

Rasha Ta Yaba Da Sakamakon Tattaunawar Iran Da Hukumar IAEA

Kasar Rasha ta yaba da sakamakon tattaunawar data wakana tsakanin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya da kuma gwamnatin Iran.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Wakilin dindindin na Rasha a kungiyoyin kasa da kasa a Vienna, Mikail Ulyanov, ya ce Moscow na maraba da sakamakon tattaunawar da akayi yayin ziyarar da shugaban hukumar ta IAEA, Raphael Grossi ya kai Tehran.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na twitter, Mista Ulyanove : ya yi fatan nan ba da jimawa ba a koma tattaunawar Vienna domi farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran ta 2015.

A ziyarar da ya kawo Tehran, Shugaban hukumar makamashin nukiliya ta duniya Rafael Grossi ya bayyana cewa, ya zama wijibi dukanin bangarori na Iran da kuma hukumar IAEA su yi aiki tare da juna.

Iran ta amince wa MDD ta sanya kyamarori a tashar Nukiliyarta, don nadar bayanan abubuwan da ke faruwa.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*