?>

Rasha Ta Mika Wa Lebanon Hotunan Tauraren Dan Adam Na Fashewar Tashar Ruwan Beirut

Rasha Ta Mika Wa Lebanon Hotunan Tauraren Dan Adam Na Fashewar Tashar Ruwan Beirut

Sama da shekara da gudanar da tagwayen fashe fashen da suka auku a tashar ruwan birnin Beirut, kasar Lebanon, ta samu hotunan tauraren dan adam na mummunar fashewar data auku.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Kasar Rasha, ce ta ya mika wa ministan harkokin wajen Lebanon din hotunan, yayin ziyarar da ya kai a Moscos.

Yayin da yake mika wa takwaransa na Lebanon hotunan, ministan harkokin wajen Rasha Sergueï Lavrov, ya ce matakin zai taimakawa Lebanon gano hakikanin abunda ya haddasa fashewar.

Hotunan kuma a cewar Mista Lavrov, an dauke su ne watannin kadan gabanin fashewar da kuma bayan ta a watan Agusta na 2020.

Fashewar da aka bayyana cewa ta auku ne sanadin ababen fashewa na ammonium Nitrat, da aka adana a wajen ta yi sanadin mutuwar mutum sama da 215 da jikkata dubbai bayan hadassa mummunar barna a birnin.

Har yanzu kuma ana bincike kan musamman fashewar, inda ake tunanin ko an harba wani abu ne wajen wanda ya hadassa fashewar.

Bayan aukuwar lamarin dai mahukuntan Lebanin sun bukaci faransa ta mika masu hotunan da tauraren dan adam dinsu ya dauka, saidai faransa ta ce tauraren dan adam din ta bai aiki wajen lokacin da lamarin ya faru, haka ita ma Amurka ba ta taimaka wa Lebanon din ba ta wannan fanin.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*