Kungiyar tarayyar Afirka (AU) ta bada sanarwan cewa gwamnatin kasar Rasha ta bawa kungiyar alluran riga kafin cutar korona samfuran Sputnic V miliyon 300. Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto John Nkengasong daraktan hukumar yaki da cututtuka na kungiyar ya na fadar haka a jiya Jumma’a.
ABNA24 : Ya kuma kara da cewa, Rasha za ta fara mika mata wadannan alluran ne daga cikin watan Mayuna wannan shekara, amma mafi yawan alluran zasu shiga hannunta ne zuwa watan Yuni.Kungiyar AU mai kasashe 55 ta na son ganin a yiwa kashi 60% na mutanen nahiyar biliyon 1.3 alluran raga kafin cutar ta korona cikin shekaru 3 masu zuwa.
Tuni dai kungiyar ta ce ta sami alluran riga kafin cutar na kamfanonin AstraZeneca, Pfizer da kuma Johnson & Johnson guda miliyon 270.
Kasashen duniya da dama sun fara amfani da alluran riga kafin cutar ta korona mai suna Spurtnik V. Kuma an tabbatar da cewa alluran tana na da inganci na kashi 91% wajen kare mutane daga kamuwa da cutar.
342/