Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - ya kawo rahoton cewa, an gudanar da karatun adduar tawassuli a haramin masallacin Jamkaran tare da jawabin Hujjatul Islam Walmuslimeen Sadiqy Waez da kuma karanta tawassuli daga bakin Haj Mehdi Mansury ya gabatar inda malamai da dama malamai, masoya da yawa da masu jiran Sayyidina Waliyul Asr (AS) suka halarta.