Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - ya kawo rahoton cewa, an gudanar da sallar idi Karama tare da halartar gungun mabiya mazhabar shi'a mabiya Ahlul Baiti (AS) a cibiyar musulunci ta Imam Montazer (AS) da ke birnin jihar Ohio dake kudu maso yammacin kasar Amurka.