Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - ya kawo rahoton cewa, ma'aikatan haramai na Imam Husaini (AS) da kuma na Sayyid Abbas (AS) sun gudanar da zanga-zangar juyayi a birnin Karbala a daidai lokacin da ake gudanar da zagayowar ranar rusa makabartar Baqiya a ranar takwas ga watan Shawwal.