?>

Ra’isi: Ya Kamata Duniya Ta Fahimci Cewa Amurka Ba Abun Yarda Ba Ce

Ra’isi: Ya Kamata Duniya Ta Fahimci Cewa Amurka Ba Abun Yarda Ba Ce

Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ibrahim Raissi ya ce Amurka ta rasa madogara, a yayin da take ikirarin neman tattaunawa a daya bangaren kuma tana kakabawa Iran sabbin takunkumai.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Shugaba Ra’isi, ya ce, kamata ya yi duniya ta fahimci cewa, ‘’ Amurka ba abun yarda ba ce’’.

Kalaman nasa sun zo ne bayan da gwamnatin shugaban Amurka Joe Biden ta sanar da kakaba sabbin takunkumai kan masana'antun sarrafa man fetur na Iran da kuma wasu kamfanonin China da UAE da Indiya da wasu mutane da Amurkar ke zarginsu da taimakawa Iran din wajen fitar da mai.

Ma'aikatar baitul malin Amurka a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce sabbin takunkuman na da nufin kara matsin lamba ne a kan Iran a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa da nufin farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran wacce ta shiga rashin tabbas.

"Idan babu wata yarjejeniya, za mu ci gaba da amfani da takunkumi don takaita fitar da man fetur daga Iran," in ji karamin sakatare na Baitulmalin Amurkar Brian Nelson, kamar yadda kafafen yada labarai suka nakalto.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*