?>

Pegasus : Manhajar Isra’ila Da Akayi Amfani Da Ita, Wajen Yi Wa ‘Yan Jarida Da Masu Fafatuka Kutse

Pegasus : Manhajar Isra’ila Da Akayi Amfani Da Ita, Wajen Yi Wa ‘Yan Jarida Da Masu Fafatuka Kutse

Wani sakamakon bincike da aka fitar, ya nuna yadda akayi amfani da wata manhajar Isra’ila, wajen yi wa ‘yan fafatukar kare hakkin dan adam da ‘yan jarida da kuma ‘yan adawa a fadin duniya kuste.

ABNA24 : Sakamakon binciken da kafofin yada labarai da dama a duniya suka rawaito, ya ce an yi amfani da manhajar ta tatsar bayanai mai suna ‘’Pegasus’’ ta kamfanin Isra’ila na NSO Group, wacce idan aka saka ta a waya za’a iya dauko sakwanni, hotuna, sunaye, kai har ma da sauraren kiraye kirayen da mai wayar ke yi.

Kamfanin na Isra’ila wanda aka kafa a 2011, ya jima yana fakewa da cewa, manhajarsa ana amfani da ita ne domin samun bayanai daga gungun masu aikata manyan laifuka ko ‘yan ta’adda.

Saidai kungiyoyi irinsu Forbidden Stories, da Amnesty International, sun ce daga shekarar 2016 sun fitar da lambobin waya na masu mu’amula da kamfanin na NSO 50,000 da aka zaba domin sanya ido akansu.

Daga cikinsu akwai ‘yan jarida 180, da ‘yan siyasa maza da mata 600, da ‘yan fafatukar kare hakkin dan adam 85, da shugabannin kamfanoni 65.

Akwai wakilai na ketare na manyan kafofin yada labarai irinsu, Wall Street Journal, CNN, RFI, France 24, Mediapart, El País, ko AFP.

Sauren sun hada da lambobin waya na wani shugaban kasa, da kuma shugabannin gwamnatoci na kasashen turai, da yarimomi, da janar-janar

Binciken ya zayyano kasashe irinsu, Mexico, Indiya, Marrocco, Saudiyya, Togo, da Hongrie, da sukayi amfani da manhajar don tatsar bayanai daga ‘yan kasarsu har ma wadanda ke a katare.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*