?>

Pegasus : Duniya Na Yin Tir Da Isra'ila Kan Yi Wa Fitatun Mutane Kutse

Pegasus : Duniya Na Yin Tir Da Isra'ila Kan Yi Wa Fitatun Mutane Kutse

Kasashen duniya da dama sun maida martani, yayin da wasu ke yin tir da yadda akayi amfani da manhajar Isra’ila wajen yi wa fitatu da kafofin yada labarai kutsen waya.

ABNA24 : Kungiyar tarayyar turai, ta bakin shugabar kwamitin kungiyar tarayyar turai ta ce babban abun damuwa ne abunda mu ke ji ana fada, idan dai har ya tabbata to zai kasance abun takaici.

A halin da ake ciki kuma kafofin labarai da daman a duniya sun shigar da karar kamfanin na Isra’ila na NSO, game batun kutsen da akayi wa ‘yan jaridunsu.

A ranar Lahadi ne Wani sakamakon bincike da aka fitar, ya nuna yadda akayi amfani da manhajar Isra’ila, Pegasus, wajen yi wa ‘yan fafatukar kare hakkin dan adam da ‘yan jarida da kuma ‘yan adawa a fadin duniya kuste.

Sakamakon binciken da kafofin yada labarai da dama a duniya suka rawaito, ya ce an yi amfani da manhajar ta tatsar bayanai mai suna ‘’Pegasus’’ ta kamfanin Isra’ila na NSO Group, wacce idan aka saka ta a waya za’a iya dauko sakwanni, hotuna, sunaye, kai har ma da sauraren kiraye kirayen da mai wayar ke yi.

Daga cikinsu akwai ‘yan jarida 180, da ‘yan siyasa maza da mata 600, da ‘yan fafatukar kare hakkin dan adam 85.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*