?>

Nijeriya: An Cafke Wani Кasurgumin Mai Garkuwa Da Mutane A Sokoto

Nijeriya: An Cafke Wani Кasurgumin Mai Garkuwa Da Mutane A Sokoto

Rahotanni daga jihar Sokoto na Nijeriya sun bayyana cewar jami’an tsaro sun sami nasarar cafke ƙasurgumin mai garkuwa da mutanen nan mai suna Bello Galadima da cibiyoyin tsaro daban-daban suke nema ruwa a jallo.

ABNA24 : Yayin da ya ke sanar da kama Bello Galadiman da jami’an hukumar Nigerian Security and Civil Defence Corps da aka fi sani da Civil Defence suka yi, daraktan hulda da jama’a na rundunar Olusola Odumosu ya ce jami’ar rundunar sun sami labarin sirri ne dangane da inda ya ke inda suka samu nasarar cafke shi kafin ya gudu.

Jami’in ya ƙara da cewa a halin yanzu dai Bello ɗin yana hannun rundunar kuma ana ci gaba da gudanar da bincike da yi masa tambayoyi. Har ila yau jami’in ya kirayi sauran masu laifi da yin garkuwa da mutane da su daina da kuma mika kansu don kuwa a cewarsa jami’an tsaro ba za su yi ƙasa a gwiwa wajen kamo su da kuma hukunta su ba. Bello Galadima dai ɗan shekaru 40 a duniya yayi ƙaurin suna wajen garkuwa a mutane a jihar Niger ta Nijeriya kafin daga baya aka ce ya koma jihar Sokoton inda aka kama shi a halin yanzu.

Tsawon shekaru biyun da suka gabata dai ya kasance cikin mutanen da jami’an tsaro suke nema ruwa a jallo.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*