?>

Nijer : A Yau Ce Ake Zagaye Na Biyu Na Zaben Shugaban Kasa

Nijer : A Yau Ce Ake Zagaye Na Biyu Na Zaben Shugaban Kasa

A yau Lahadi ne masu zabe zasu kada kuri’unsu a karo na biyu don zaben shugaban kasa a jumhuriyar Niger. Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa yan takara guda biyu wadanda suka sami mafi yawan kuri’u a zagaye na farko ne zasu yi takara a zaben na yau, kuma sune Bazoum Muhammad na Jam’iyyar gwamnati ma ice da kuma tsohon shugaban kasar Mamman usaman.

ABNA24 : A zagaye na farko da Bazoum ya sami kasha 39.3% na yawan kuri’un da aka kada, a yayinda wanda yake biye masa wato Mohammad Usman yake da kasha 17% na yawan kur’in da aka kada.

A zaben nay au dai yan takara wadanda suka zo na ukku da hudu duk suna goyon bayan Zaboum Muhammad wanda wasu suke ganin shi zai lashe zaben.

Bazoum, dan shekara 61 ya rike mukamai da dama a gwamnati mai wadanda suka hada da ministan harkokin waje da kuma na cikin gida. Kuma yay i alkawarin zai ci gaba da tsaron shugaban kasa mai ci wato Muhammad yusuf wanda wa’adinsa yake karewa.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni