?>

Yan Hakika Ba 'Yan Tijjaniyya Ba Ne, masu bin akidar shedan  ne:

Yan Hakika Ba 'Yan Tijjaniyya Ba Ne, masu bin akidar shedan  ne:

Cewar wani malamin darika da ya nemi a sakaya sunan sa a kaduna.

Daga Aliyu muhammad,kaduna

wannan malami ya fa da acikin firarsa cewa shehu Dahiru usman Bauci ya fada a wata fira da yayi da manema labarai cewa.


...kaf Nijeriya babu wanda ya kai mabiyan Tijjaniyya yawan mahaddata Kur'ani mai girma cewarsa,


Malamin yace akwai musulmi da yawa a Najeriya da suke aikata kaba'irai iri iri kamar

 Shan Giya,  Neman Mata, Sata,  Karya,  Luwadi, Caca,  Madigo, Suna Aikata Laifuka Mabanbanta Wanda Aka Sani Da Wanda Ba'a Sani Ba, to amma

Musulunci Ne Ya ce Su yi Hakan? Kowa  nasan  zaice min A'a. To me yasa idan an samu wasu bata gari daga cikin mu suna bata Sunan Darikar tijjaniyya sai wasu marasa adalcin suce haka koyarwar darikar tijjaniyya  take?


Kowa dai ya sani a Najeriya dama duniya baki daya masu bin koyarwar shehu Ibrahim Inyas da abinda aka sansu da shi,


* Istigfari,

* Salatin ANNABI (S.A.w), Da

* La'ilaha Illallahu,

* Kulawa Da Sallar Jam'i,

* Girmama Iyaye Da Yimusu Biyayya,

* Yawan Karatun Qur'ani.


Da sauran abubuwa na ibada inji shi


 Shi ya sa a Nijeriya Babu Wanda Ya Kai 'Yan Tijjaniyya Na Gaskiya yawan mahaddata Alkur'ani mai girma, Ba 'yan tijjaniyya shedaniyya ba.


malamin yace irin wadannan Bara gurbin Darikar tijjaniyyar ba tare muke da akidar su ta Hada Allah subahanahu wa ta'ala da shehu ibrahim inyas ba Malamin yace shehu ibrahim mutun ne malami bawan Allah bawai Allah ba kamar yadda wadannan shedanun suke fada.


Daga karshe malamin yayi kira ga Gwamnati da tasa idanu akan irin wadan nan shedanun domin cafkesu a duk inda suke dan yimusu hukunci.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*