?>

Najeriya:Gwamnati Ta Shigar Da Sabbin Kararraki Kan Sheikh Ibrahim El-Zakzaky

Najeriya:Gwamnati Ta Shigar Da Sabbin Kararraki Kan Sheikh Ibrahim El-Zakzaky

Gwamnatin Jihar Kaduna a tarayyar Najeriya ta bada sanarwar shigar da sabbin kararraki kan shugaban harka Islamiyya ko (IMN) wato Sheikh Ibrahim Elzakzaky da matarsa Malama Zeenat.

ABNA24 : Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto Dari Bayero daractan kula da kararraki na jihar Kaduna ya na fadar hakan a yau Asabar ya kuma kara da cewa gwamnatin jihar ba ta gamsu da hukuncin da babban kotu a jihar ta yanke na wanke Malamin da kuma matarsa a cikin ‘yan kwanaki da suka gabata ba.

Har’ila yau Bayero ya kara da cewa a cikin sabbin kararraki da suka shigar kan Sheikh Ibrahim El-zakzaky, a wannan karon sun hada da tuhumar aikata ta’addanci, taimakawa makiyan gwamnati da kuma wasu laifuffuka na daban.

Kwanaki biyu kenan da wanke su daga aikata wani laifi da kuma sallamarsu wanda wata babban kotu a kaduna tayi.

Tun shekara ta 2015 ne gwamnatin jihar Kaduna take tsare da Sheikh El-Zakzaky da matarsa bayan wani dirar mikiya wanda sojojin kasar suka yi a kan gidan sa a birnin Zariya, inda suka kashe akalla mutane 350. Sannan suka kama wasu daruruwa.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*