?>

Najeriya : Wasu Ɗaliban Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Zamfara Sun Gudu Daga Hannu Masu Garkuwa Da Su

Najeriya : Wasu Ɗaliban Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Zamfara Sun Gudu Daga Hannu Masu Garkuwa Da Su

Rahotanni daga jihar Zamfara da ke Nijeriya sun tabbatar da cewa wasu ɗalibai guda biyu na makarantar sakandaren birnin Yawuri da ke jihar Kebbi sun sami tsira daga hannun ‘yan bindigan da suka sace su, sai dai kuma ana ci gaba da samun rashin tabbas kan yadda aka yi suka tsiran.

ABNA24 : Tun da fari dai wasu rahotanni sun ce mazauna garin Dandalla ne suka tsinci waɗannan ɗaliban a dajin Dansadau na ƙaramar hukumar Maru ta Jihar Zamfara jiya Asabar. Rahotannin sun ce daga nan ne mutanen garin suka miƙa waɗannan yaran ga ‘yan sanda a garin na Ɗansadau inda aka wuce da su zuwa helkwatar ‘yan sanda da ke garin Gusau babban birnin jihar Zamfaran.

To sai dai kuma daga bayan rundunar 'yan sandan Jihar Zamfaran ta ce ita ce ta ceto ɗaliban biyu da 'yan bindiga suka sace a watan Yunin da ya gabata.

Yayin da ya ke sanar da hakan a wata ganawa da yayi da manema labarai a yau Lahadi, Kwamishinan 'Yan Sandan jihar Zamfara Husaini Abubakar ya ce jami'an ‘yan sandan ne suka yi ceto ɗaliban biyu wato Faruk Buhari mai shekara 17 da Maryam Abdulkarim mai shekara 15.

A ranar 17 ga watan Yunin da ya gabata ne dai wasu 'yan bindiga suka kutsa makarantar sakandaren ta garin Yawuri da ke jihar Kebbi inda suka sace ɗalibai sama da 30 da wasu malaman makarantar, bayan wani gumurzu da sojoji inda sojojin suka sami nasarar kashe wani adadi mai yawa na maharani da kuma ceto wasu daga cikin ɗaliban.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*