?>

Najeriya: Mai Yiyuwa A Dawo Da Dokar Hana Fita A Wasu Jihohi Sanadiyar Covid-19

Najeriya: Mai Yiyuwa A Dawo Da Dokar Hana Fita A Wasu Jihohi Sanadiyar Covid-19

Yawan wadanda suke kamuwa da cutar Covid-19 a tarayyar Najeriya yana karuwa a hankali, wanda ya sa wasu masana suke ganin mai yiyuwa wannan ya tilastawa gwamnatin tarayyar kasar sake maida dokar hana fita a wasu garuruwa nan gaba.

ABNA24 : Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto hukuma mai kula da cututtuka masu yaduwa ta kasa NCDC a shafinta na face book tana cewa mutane 590 ne suka kamu da cutar ta Covid 19 a duk fadin kasar a jiya Jumma’a a yayinda wasu mutane 8 suka rasa rayukansu sanadiyyar cutar.

Wannan ya kawo adadin wadanda suka kamu da cutar tun bayan bullarta a kasar a shekarar da ta gabata zuwa 173,411.

Labarin ya kara da cewa cutar ta fi yaduwa a cikin jihohi 17 da kuma Abuja babban birnin kasar a wannan karon.

Labarin ya kammala da cewa, hana fita ko takaida shi da akayi a baya dai ya gurgunta tattalin arzikin kasar, wanda har yanzu wasu harkokin kasuwansu basu murmure daga garesu ba.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*