?>

Najeriya: Lauyoyin Sheikh Zakzaky Za Su Dauki Matakai Kan Yunkurin Sake Gurfanar Da Shi

Najeriya: Lauyoyin Sheikh Zakzaky Za Su Dauki Matakai Kan Yunkurin Sake Gurfanar Da Shi

Lauyoyin Sheikh Ibrahim Zakzaky Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya a shirye suke su dauki duk wani mataki da ya dace bisa tsarin shari’a, dangane da yunkurin gwamnatin Kaduna na sake gurfanar da shi.

ABNA24 : Kotun jihar Kaduna ta sanar da hukuncinta na karshe ne dangane da shari’ar Sheikh Ibrahim Zakzaky da maidakinsa malama Zinat Ibrahim a ranar 28 ga watan Yulin da ya gabata, da ke tabbatar da cewa babu gamsassun dalilai kan laifukan da ake zarginsu da aikatawa, kuma kotun ta sanar cewa ta sake su.

To sai dai a nata bangaren gwamnatin jihar Kaduna karkashin shugabancin gwamnan jihar Nasir Elrufa’i, ta sanar da cewa ba ta gamsu da hukuncin babbar kotun jihar ba.

Bayan hakan gwamnatin jihar ta sake tsara wasu tuhumce-tuhumce na daban da nufin sake kai karar sheikh Ibrahim Zakzaky a kotu, domin ganin cewa an ci gaba da tsare shi.

To sai dai a nasu bangaren lauyoyin Sheikh Zakzaky sun bayyana hakan da cewa, ba zai hana su ci gaba da daukar nasu matakan ba, daidai da abin da yake cikin tsarin shari’a ta Najeriya.

Barr Ishaq Adam daya ne daga cikin manyan lauyoyi da suke kare Sheikh Ibrahim Zakzaky, ya bayyana cewa batun sake tsara tuhumce-tuhumce ko daukaka kara abu ne wanda an saba jin sa a cikin lamarin shari’a, saboda haka su ana su bangaren suna da nasu matakan za su bi kan wannan batu.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*