?>

Najeriya: Kotu Ta Bayar Da Dama Ga Sheikh El-Zakzaky Da Ya Tafi Waje Neman Magani

Najeriya: Kotu Ta Bayar Da Dama Ga Sheikh El-Zakzaky Da Ya Tafi Waje Neman Magani

Kotun koli da take a jahar Kaduna, a zaman da ta yi ayau Litinin ta yanke hukunci akan bayar da dama ga shugaban harkar musulunci a Najeriya, Sheikh Ibrahim Yakubu El-zakzaky da ya tafi kasar India neman magani kamar yadda ya bukata

(ABNA24.com) Kotun koli da take a jahar Kaduna, a zaman da ta yi ayau Litinin ta yanke hukunci akan bayar da dama ga shugaban harkar musulunci a Najeriya, Sheikh Ibrahim Yakubu El-zakzaky da ya tafi kasar India neman magani kamar yadda ya bukata

Sai dai shehun malamin da mai dakinsa, Zeenat ba su sami halartar zaman kotun na yau ba a lokaci da aka yanke hukunci.

Gabanin bude zaman shari’ar, an baza jami’an tsaro a kan muhimman titunan birnin Kaduna.

An rufe babban titin Ahmadu Bello a daidai lokacin da ake dakon fara shari’ar.

Tun a shekarar 2015 ne dai ake tsare da Sheikh Ibrahim Yakubu El-Zakzaky bayan wani hari da sojojin kasar su ka kai wa gidansa a cikin birnin Zaria. A yayin wancan harin dai an kashe daruruwan magoya bayan Sheikh Ibrahim Yakubu El-Zakzaky, kamar kuma yadda aka rusa ginin Husainiyyar Bakiyyatullah./129


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*