?>

Najeriya: Jami’an Tsaro Sun Kama Wasu ‘Isra’ilawa’ Bisa Zargin Alaƙa Da ‘Yan Кungiyar IPOB

Najeriya: Jami’an Tsaro Sun Kama Wasu ‘Isra’ilawa’ Bisa Zargin Alaƙa Da ‘Yan Кungiyar IPOB

Rahotanni daga Najeriya sun bayyana cewar jami’an tsaron farin kaya na ƙasar DSS sun kama wasu ‘masu shirya fina-finai’ da ‘yan Isra’ila su uku bisa zargin alaƙa da haramtacciyar ƙungiyar nan ta IPOB mai ƙoƙarin kafa ƙasar Inyamurai zalla ta Biafra.

ABNA24 : Jaridar Times ta Isra’ilan ce ta fara ba da labarin inda tace jami’an tsaron DSS ɗin sun kama mutane da kuma yi musu tambayoyi kan zargin da ake yi suna da alaƙa da ‘yan ƙungiyar awaren ta IPOB.

Isra’ilawan da jami’an tsaron suka tsare sun hada da Rudy Rochman, sanannen bayahude mai tsananin ra’ayin sahyoniyanci da kuma Noam Leibman mai shirya fina-finai sai kuma wani ɗan jarida E. David Benaym.

An ce dai Isra’ilawan sun zo Najeriya ɗin ne don shirya wani fim mai suna ‘We Were Never Lost’ da zai yi magana kan yahudawa da suke ƙasashen Afirka irin su Kenya, Madagascar, Uganda da kuma Nijeriya.

Jami’an na DSS sun kama su ne a wani kauye mai suna Ogidi da ke jihar Anambra inda suka tafi da su helkwatarsu da ke Abuja don ci gaba da gudanar da bincike a kansu.

An jima dai ana zargin Isra’ila da hannu cikin irin abubuwan da ƙungiyar ta IPOB da shugabanta Nnamdi Kanu, wanda a halin yanzu ake tsare da shi, suke aikatawa na tashin hankali da kashe-kashe a Najeriyan.

Kanu ɗin wanda a wani lokaci a baya ya kai ziyara Isra’ila da kuma ganawa da wasu jami’ai a can ya jima yana nuna ‘yan kabilar Igbo a matsayin yahudawa.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*