?>

Najeriya : EFCC Ta Kama Tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa Da Matarsa

Najeriya : EFCC Ta Kama Tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa Da Matarsa

Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa a tarayyar Najerita ta na tsare da tsohon gwamnatin Jihar Nasarawa Tanko Al-Makura da matarsa Mairo saboda zargin almundahana da dukiyar jama’a.

ABNA24 : Wata majiyar hukumar ta shaidawa jaridar Premium times ta Najeria kan cewa a halin yanzu tsohon gwamnan da matarsa suna tsare a cibiyar hukumar dake Abuja babban birnin kasar.

Majiyar ta kara da cewa zargin da akewa tsohon gwamnan ya shafi wasu makudan kudade na gwamnatin Jihar ta Nasarawa wadanda shi da matarsa suka wawura ta wasu hanyoyin da basu dace ba.

Almakura ya zama gwamna na tsawon shekaru 8 a jihar Nasarawa, wato daga shekra ta 2011 zuwa 2019, kafin a zabeshi a kan kujerar sanata mai wakiltar Nasarawa ta kudu.

Premium times ta kara da cewa wannan dai shi ne karon farko wanda hukumar ta ke zargin tsohon gwamnan da almundahana da kudaden jama’a.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*