?>

Najeriya : Babu Wanda Ya Tsira Daga Hatsarin Jirgin Saman Soji A Abuja

Najeriya : Babu Wanda Ya Tsira Daga Hatsarin Jirgin Saman Soji A Abuja

Rundunar sojin saman Najeriya, ta ce babu wanda ya tsira daga hatsarin jirgin saman soji da ya fara yau Lahadi a birnin Abuja.

ABNA24 : Da yake sanar da hakan kakakin rundunar Air Vice Marshal Ibikunle Daramola, ya ce dukkanin mutum bakwai da ke cikin jirgin basu tsira daga hatsarin ba.

Babu dai karin bayyani daga rundinar game da musababin hatsarin jirgin, amma tuni babban hafsan sojin sama na kasar ya bayar da umurnin kaddamar da bincike kan musabbabin hatsarin.

Amma a nasa bangare ministan sufurin jiragen sama na kasar, Hadi Sirika ya ce jirgin mai suna King air 350 ya yi hatsari ne bayan ya samu matsalar na'ura a lokacin da ya tashi sama, kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter.

Bayanai sun ce jirgin yana cikin wadanda Najeriya ta sayo domin ayyukan tsaro da leken asiri.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni