?>

Najeriya: An Dage Shari’ar Nnamdi Kanu Zuwa Watan Oktoba Mai Zuwa

Najeriya: An Dage Shari’ar Nnamdi Kanu Zuwa Watan Oktoba Mai Zuwa

An dage shari’ar da ake yi wa Nnamdi Kanu shugaban kungiyar IPOB mai rajin ballewa daga Najeriya zuwa rana 21 ga watan Oktoba mai zuwa.

ABNA24 : Shafin yanar gizo na ‘Africa News’ ya nakalto wani lawyan Kanu ya na haka, ya kuma kara da cewa mai shari’ar ta dage shari’ar zuwa ne saboda ta ce, ba za ta fara sauraron shari’ar ba tare da wanda ake kawo kara.

Kafin haka dai ministan Shariar kasar ta Najeriya Abubakar Malami ya ce ana tuhumar Kanu da laifuffuka wadanda suka hada da ta’addanci,mallakar kamfani ba bisa ka’ida ba, mallakar makamai da kuma wallafa wasu bayanan karya.

An fara kama Kanu ne a shekra 2015, sannan ya tsallaka belin da aka bashi a shekara ta 2017, daga karshe an kamoshi daga kasashen waje aka dawo da shi gida a cikin watan Yunin da ya gabata.

Kafin akama shi dai magoya bayansa a yankin kudu masu gabacin tarayyar Najeriya inda ‘yan kabilarsa IBO suka fi yawa sun kashe jami’an tsaro da dama, sun kuma kona ofisoshin yansanda da kuma na hukumar zabe a yankin.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*