?>

Mutanen Yamen Sun Yi Zanga-Zanar Yin Tir Da Goyon Bayan Da Amurka Ke Bawa Saudiya

Mutanen Yamen Sun Yi Zanga-Zanar Yin Tir Da Goyon Bayan Da Amurka Ke Bawa Saudiya

Rahotanni da muka samu daga kasar Yamen sun bayyana cewa dubu dubatan Al’ummar kasar ne suka bazu akan titunan manyan biranen kasar domin yin Allah wadai da hadin guiwar da Amurka ta ke yi da Saudiya a ci gaba da yakin da ta kaddamar kan kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : A tsakiyar birnin Sa’ada dubban masu zanga - zangar dauke da tutocin kasar sun ta rera taken yin Allah wadai da Amurka da Saudiya tare da dora alhakin dukkan matsalar tattalin arziki da hare-haren soji da wurga kasar cikin yakin basasa kan Amurka

Ana sa bangaren Yahaya Omran gwamnan rikon kwarya a lardin Sa’ada ya fadi a lokacin zanga-zangar cewa Amurka da abokiyar burminta wato HKI itace babbar mai taimakawa kasar Saudiya a ci gaba da kai hare-hare kan Asibitoci da makarantu da gidajen fararen hula da dakarun kawance da Saudiya ke jagoranta ke kai wa a kasar.

Daga karshe ya ce gwamnatin Joe biden da sauran kawayenta a yankin sun ci gaba da taimakawa saudiya a bangaren soji da siyasa domin samun karfin guiwa na ci gaba da hare-haren zalunci kan Alummar kasar yamen .

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*