Ziyarar Trump A HK.Isra'ila

Ziyarar Trump A HK.Isra'ila

A ci gaba da ran gadinsa na farko a wasu kasahen duniya, shugaban Donald Trump na Amurka ya isa Isra'ila a yau Litinin.

Daya daga cikin batutuwan da ake sa ran Trump zai dauko har da batun farfado da tattaunawar neman zamen lafiya tsakanin mahukuntan yahudawan mamaya na Isra'ilar da kuma na Palasdinu.

Kafin isar Mista Trump dai Isra'ila ta kaddamar da wani shiri na sassautawa al'ummar Falasdinu.

A gobe ne kuma ake sa ran Trump zai ziyarci yankin al'ummar Palasdinu da yahudawan ke ci gaba da mamayewa.

A jiya ne dai shugaba Trump ya kammala wata ziyarar ta kwanaki biyu a Saudiyya.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky