Zarif: Iran Tana Da Masaniya Kan Shirin Saudiyya Na Kashe Manyan Jami'an Iran

Zarif: Iran Tana Da Masaniya Kan Shirin Saudiyya Na Kashe Manyan Jami'an Iran

Ministan harkokin wajen kasar Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewar Iran tana sane da makircin da Saudiyya take kullawa na kashe manyan jami'an kasar Iran.

Ministan harkokin wajen na Iran ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da jaridar al-Araby al-Jadeed ta kasar Qatar inda ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da masaniya kan wannan shiri da Saudiyya take da shi na kashe manyan jami'an kasar.

Ministan harkokin wajen na Iran yayi karin haske dangane da wasu daga cikin aika-aikan da gwamnatin Saudiyya din take aikatawa cikinsu kuwa har da irin goyon bayan da take ba wa ayyukan ta'addanci a duniya, harin wuce gona da iri da take ci gaba da kai wa kasar Yemen, killace kasar Qatar da ta yi bugu da kari kan yin garkuwa da firayi ministan kasar Labanon Saad Hariri da ta yi a kwanakin baya.

Mr. Zarif yana mayar da martani ne dangane da wani rahoto da jaridar New York TImes ta buga dangane da wani taro da mahukutan Saudiyyan karkashin jagorancin yarima mai jiran gado na kasar Muhammad bin Salman don tsara yadda za a kashe wasu manyan jami'an kasar Iran ciki kuwa har da kwamandan dakarun Qudus na Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci na Iran din Manjo Janar Qassem Soleimani.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni