Zamu daukaka kara Inji Sheikh Yakubu Yahaya Katsina

Zamu daukaka kara    Inji Sheikh Yakubu Yahaya Katsina

Sheikh Yakubu Yahaya Katsina ya bayyana cewa zasu daukaka kara dangane da hukuncin da Alkalin babban kotun tarayya na Kaduna yayi na watsi da karar da Sheikh Ibrahim Zakzaky ya shigar a kotun yana neman haqqoqinsa a kotun.

Sheikh Yakubu Yahaya ya bayyana haka ne a jiya talata lokacin da yake jawabi a markaz din ‘yan uwa na Katsina na jan hankali ga ‘yan uwa akan abubuwan da ya kamata su lura dashi dangane da wannan hukunci na kotun Kaduna.
Malamin yace idan ‘yan uwa bacci suke yi ya kamata su farka akan raunin da suka yin a addu’o’i na yau da kullum saboda har yanzu ana tsare da su Sheikh Zakzaky ba bisa doka ba,ba kuma tare da laifin komai ba.
A lokacin da yake bayani dangane da hukuncin kotun na Kaduna sai yace:
“Kotu tace duk abinda aka yi mana a Zariya karya ne, ba a yi mana komi ba,duk karya ne.Ba a rusa gidan Malam ba,ba a rusa Husainiyyah ba,ba su yiwa Malam komai ba.Ba su kashe kowa ba,ba abinda aka yi mana.Wannan shine abinda kotun Kaduna ta fada.
“Zaluncin da aka yi mana a fili yake.Shari’ar Abuja daban take,ta Kaduna ma daban take amma Alkalin kotun Kaduna yace duk abu guda daya ne.Da suke cewa akwai doka da oda a kasar nan karya ce,babu wata doka saboda kotu ta bada hukunci a Abuja amma sun ki su bi dokar.”
Malamin yayi kira ga ‘yan uwa da su dauki nasarar da suka samu a Abuja a matsayin Badar.Sannan ka da su samu rauni da wannan hukunci na Kaduna saboda zasu daukaka kara kuma zasu je duk in da ya kamata su je domin neman haqqinsu.
Ya nuna anyi haka ne domin a gani ko zasu yi hargitsi da yamutsi,saboda haka ka da ‘yan uwa su bari ayi amfani da su wajen aiwatar da wannan nufi na azzulumai.
A karshe yayi kira  gan ‘yan uwa da su taimaka saboda a yanzu haka a asusun su babu komai kuma dukkan abubuwan da ake yi na kudi ne,saboda haka a taimaka da duk abinda za a iya taimakawa.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Shahadar Kwamandojin Musukunci. Haj,Kasim Sulemani Da Abu Mahdi
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni