Za'a Bude Ofishin Kula Da Bukatun Kasar Iran A Saudia Don Kula Da Mahajjata

Za'a Bude Ofishin Kula Da Bukatun Kasar Iran A Saudia Don Kula Da Mahajjata

Shugaban hukumar Hajji Da Ziyara ta kasar Iran ya bada sanarwan bude ofishin kula da bukatun Iraniyawa a kasar Saudia don kula da bukatun mahajjata da kuma masu zuwa umra da ziyara.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Mohammad Muhammadi shugaban hukumar Hajji da Ziyara yana fadara haka a safiyar yau litinin ya kiuma kara da cewa ma'aikata masu kula da mahajjata da masu ziyara Iraniyawa fiye da 300 ne zasu taimakawa mahajjata a aikin hajjin bana.

Muhammadi ya kara da cewa kashi 75% na mahajjatan Iran a hajjin bana tsoffin ne yan sama da shekaru 50, don haka ne aka zabi kwararrun likitoci 300 don kula da su a lokacin aikin hajjin bana. Sauran ma'aikatan sun hada da jami'an bada agaji, masu khidimar abinci, ma'aikatan zirga zirga, wuraren zama da kuma likitoci da jami'an jinya.

Daga karshe Muhammadi ya kammala da cewa Iraniyawa dubu 85,200,000 ake saran zasu sauke faralin aikin hajja a bana. Kuma za'a fara jigilarsu ne a ranar 18 ga watan Yuli mai kamawa zuwa kasa mai tsarki daga tashoshin jirage sama 20 a duk fadin kasar.

 


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky