Yemen: Saudiyya Ta Yi Kisan Kiyashi A Garin al-Hudaida

Yemen: Saudiyya Ta Yi Kisan Kiyashi A Garin al-Hudaida

Jiragen yakin Saudiyya sun kai hari a asibitin al-thaurah da ke garin al-Hudaidah, wanda ya yi sanadin shahadar mutane da dama

Tashar talabijin din al-masirah ta kasar Yemen ta ba da labarin cewa: Bayan harin da jiragen yakin na Saudiyya su ka kai akan asibitin, sun kuma kai wasu hare-haren a cikin unguwannin birnin wanda kawo ya zuwa yanzu mutane 26 ne su ka yi shahada yayin da wasu 35 suka jikkata.

Tashar talabijin din al-Mayadeen da ke Lebanon ta bayyana abin da ya faru da kisan kiyashi.

Bugu da kari jiragen yakin Saudiyyar sun kai wa mausnta hari a garin na Hudiadai tare da kashe da dama daga cikinsu.

Saudiyya ta tsananta kai hare-hare akan fararen hular kasar Yemen a cikin kwanakin nan, saboda rufe kashin da suke sha a hannun sojoji da dakarun sa-kai na Yemen.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Prophet's birthday celebrations
We are All Zakzaky