'Yan Tawayen Sudan Ta Kudu Sun Amince Da Raba Madafun Iko Tsakaninsu Da Gwamnatin Kasar

'Yan Tawayen Sudan Ta Kudu Sun Amince Da Raba Madafun Iko Tsakaninsu Da Gwamnatin Kasar

Ministan harkokin wajen kasar Sudan ya sanar da cewa: 'Yan tawayen Sudan ta Kudu sun amince da mika ragamar mataimakin shugaban kasa ga jagoransu Riek Machar a karkashin yarjejeniyar sulhu da aka cimma a kasar.

A bayan zaman tattaunawan sulhu da ya gudana a kasar Uganda kan rikicin kasar Sudan ta Kudu a jiya Asabar tawagar da ke shiga tsakani a ta bakin ministan harkokin wajen kasar Sudan al-Dirdiri Muhammad Ahmad ya bayyana cewa: 'Yan tawayen Sudan ta Kudu sun amince da shirin raba madafun iko tsakaninsu da bangaren gwamnatin kasar, inda madugun 'yan twayen Riek Machar zai sake rike ragamar mataimakin shugaban kasa na farko a kasar.

Al-Dirdiri Muhammad Ahmad ya kara da cewa: Shugaban kasar Sudan ta Kudu Silva Kiir zai ci gaba da rike ragamar shugabancin kasar tare da mataimaka hudu, biyu daga cikinsu daga bangaren 'yan tawaye wato Riek Machar da wata mace.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky