'Yan Takarar Shugabancin Kasar Iran Sun Gudanar Da Muhawara Ta Biyu

'Yan Takarar Shugabancin Kasar Iran Sun Gudanar Da Muhawara Ta Biyu

Yan takarar shugabancin kasar Iran sun gudanar da muhawara karo na biyu a jiya, domin bayyana irin tsare-tsaren da kowannesu yake da shi idan ya samu nasarar lashe zabe.

'Yan takarar 6 su ne; Hassan Rauhani, Ibrahim Ra'isi, Mustafa Agha Mirsalim, Muhammad Bakir Qalibaf, Musatafa Hashimi Taba, Ishaq Jihangiri.

Dukkanin 'yan takarar sun gabatar da bayani daidai wa'adin lokacin da aka kayyade musu, tare da amsa tambayoyi a kan shirin nasu, sannan kuma sun bayyana mahagansu dangane da tsaron kasa, tsarin da kuma al'adun jumhoriyar musulinci ta Iran, ci gaban ilimi da kuma fadadar shi, shirin Nukiliyar Iran na zaman lafiya, batun takunkumin da kasar ke fuskanta da kuma mahimancin da su baiwa harakokin siyasar waje.

A makun da ya gabata ne 'yan takarar shugaban kasar ta Iran Shida suka gudanar da muhawarar farko ta kai tsaye a gidajen telbijin na kasa, kuma a maku mai zuwa ne za su gudanar da muhawara ta uku kuma ta karshe.

Wannan dai shi ne karo na 12 da za a gudanar da zaben shugaban kasa a Iran tun bayan samun nasarar juyin juya halin muslunci a cikin shekara ta 1979, zaben shugaban kasar Iran mai zuwa zai gudana ne a ranar 19 ga watan Mayu mai kamawa.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky