Yan Ta'adda Sun Kashe Dakarun Tsaron Kan Iyakar Kasar Iran 10

Yan Ta'adda Sun Kashe Dakarun Tsaron Kan Iyakar Kasar Iran 10

Wasu gungun 'yan ta'adda sun kaddamar da harin wuce gona da iri kan dakarun tsaron kan iyakar kasar Iran a lardin Sistan wa Baluchestan a shiyar kudu maso gabashin Iran.

Kakakin rundunar tsaron kasar Iran Sa'id Muntazar Mahdi ya bayyana cewa: A cikin daren jiya Laraba wasu gungun 'yan ta'adda sun kaddamar da harin wuce gona da iri kan dakarun tsaron kan iyakar kasar Iran a lardin Sistan wa Baluchestan da ke shiyar kudu maso gabashin Iran kusa da kan iyaka da kasar Pakistan lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar dakarun tsaron Iran 10 tare da jikkatan wasu na daban.

Sa'id Muntazar ya kara da cewa: Harin ya yi sanadiyyar mutuwan dakarun Iran takwas ne nan take, sannan bayan kai wadanda suka samu raunuka asibiti wasu karin biyu suka rasa rayukansu saboda tsananin raunuka da suka samu.

Wasu gungun 'yan ta'adda da suke adawa da tsarin Musulunci a kasar Iran da suke da matsuguni a cikin kasar Pakistan sun dauki alhakin kai harin na jiya.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky