Yan Ta'adda Fiye Da 10,000 Ne Suka Kwararo Cikin Afrika

Yan Ta'adda Fiye Da 10,000 Ne Suka Kwararo Cikin Afrika

Ministan harkokin wajen kasar Moroko ya bayyana cewa: Akwai 'yan ta'adda da suka haura 10,000 da suka shigo cikin kasashen nahiyar Afrika

A jawabinsa a zaman taro kan gudanar da bincike dangane da barazanar 'yan ta'adda a nahiyar Afrika da ake gudanarwa a kasar Moroko: Ministan harkokin wajen kasar ta Moroko Nasser Bourita ya yi furuci da cewa: A halin yanzu haka akwai gungun 'yan ta'addan kasa da kasa da yawansu ya haura 10,000 daga kungiyoyin ta'addanci na Da'ish da Al-Qa'ida a cikin kasashen nahiyar Afrika.

Nasser Bourita ya kara da cewa: Gungun 'yan ta'addan suna ci gaba da kaddamar da hare-haren wuce gona da iri a sassa daban daban na nahiyar, kuma hare-haren da suka kai wa ya haura irin wadanda suke kai wa a kasashen yammacin Turai.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky