?>

Yan Shi’a Mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky Sun Yi Taro Domin Wafatin Manzon Allah (sawa) A Fadin Tarayyar Nijeriya

Yan Shi’a Mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky Sun Yi Taro Domin Wafatin Manzon Allah (sawa) A Fadin Tarayyar Nijeriya

Jiya Juma’a tayi daddai da 27 ga watan Safar a lissafin wata a Nijeriya wadda a irin wannan ranar ce Manzon Allah (SAAw) ya bar duniya zuwa ga Allah Subhanahu wa Ta’ala. Sananne tsakanin musulmi ‘yan shi’a a duk inda suke suna zama suna raya wannan rana da addu’o’I da ziyarori da karanta siran Annabi (saw) domin daukan darasi.
Mabiya Sheikh Zakzaky Kaman sauran ‘yan uwansu ‘yan shi’a na duniya sun gabatar da wannan taro a wurare da dama a fadin tarayyar Nijeriya.
Sheikh Adamu Tsoho Jos a lokacin da yake bayani a wajen taron garin Jos ya tattauna abubuwa masu yawa dangane da wasicin Annabi (saw), yayi bayanin abubuwan da suka faru a Hajjin bankwana da yanda Annabi ya kalifantar da Imam Ali a Ghadeer.
Shehin Malamin ya tabo batun rundunar Usama wadda Manzon Allah ya kawwana ya sanya Usama ya jagoranci Sahabbai zuwa Yemen, da rashin bin Umurnin Manzon Allah na fita tare da Usama zuwa Yemen da Sahabbai suka yi. Malamin yayi bayani dangane da rashin lafiyar Annabi a karshen rayuwarsa da abubuwan da suka faru a Raziyatu Yaumil khamis inda Sahabbai suka saba umurnin Manzon Allah na bashi tawada da abin rubutu a lokacin da ya bugace su da su bashi takarda da abin rubutu domin ya rubuta masu abinda idan suka rike shi ba zasu halaka ba har abada.
Shi kuma Sheikh Sanusi Abdulkadir a lokacin da yake gabatar da jawabin a taron tunawa da wafatin Annabi a garin Kano yayi bayyana cewa wannan rana ce da bakin ciki da jajantawa ‘yan uwa musulmi. Sannan yayi bayani dangane da muhimmancin rubuta wasiya inda yake cewa a mazhaban Ahlulbait wajibi ne yin wasiya, ko a fadawa amintattu ko a rubuta a ajiye, amma rubutawa ya fi muhimmanci.
Malamin ya bayyana cewa wasiyyar Manzon Allah ta kasu kashi kashi ne; Akwai wadda Manzon Allah yayi a ranar Arfa, da wadda yayi a ranar Gadeer, da kuma wadda yayi a lokacin da ya kwanta rashin lafiyar ajali. Idan a koma jawabin malamin za a ji yanda yayi bayani dalla dalla dangane da wadannan wasiyoyi na Annabi kafin ya bar duniya a 27 ga Safar.
Sheikh Yakubu Yahaya ya bayyana cewa sau biyu ana ba Annabi guba a lokacin da yake jawabi a wajen taron tunawa da ranar wafatin Manzon Allah a Markazin almajiran Sheikh Zakzaky dake Katsina. Yana cewa “ An ba Annabi guba har sau biyu; Na farko, wata mata Bayahudiyya ta bashi guba cikin cinyar Akuya. Na biyu kuma, wasu mutane har da manyan Sahabbai ne suka sanya ma Annabi guba a cikin magani, sun bashi yace su sha ya gani, duk da haka sai da suka sanya mashi har ta zama sanadiyyar wafatin Annabi (saw)”
Ayi irin wannan taro a garuruwan da suka hada Zariya, Bauci, Sokoto, Kauran Namoda da sauransu

Nigeria

Nigeria

Nigeria

Nigeria

Nigeria

Nigeria

Nigeria

Nigeria

Nigeria

Nigeria

Nigeria

Nigeria

Nigeria

Nigeria

Nigeria


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*