Yan Sanda Sun kaiwa masu Mazaharar A  Saki Sheikh zakzaky Hari a Kaduna:

Yan Sanda Sun kaiwa masu Mazaharar A  Saki Sheikh zakzaky Hari a Kaduna:

Daga Aliyu Muhammad,kaduna


A yau laraba ne 'yan uwa Almajiran sheikh Ibrahim zakzaky suka shirya wata ga garumar zanga zangar lumana domin nuna rashin amincewar su da tsare  jagoran na su sheikh ibrahim zakzaky,  malam Aliyu tirmuzi shine wakilin 'yan uwa Almajiran sheikh zakzaky a Kaduna kuma ya yiwa 'yan jarida Karin haske da cewa, "muna cikin muzaharar mu ta kiran a sakan mana jagoran mu sheikh ibrahim zakzaky lami lafiya kawai sai mukaji 'yan sanda sun bude mana wuta da harsha shai  masu rai, nan take suka harbi mutane da dama, kuma suka kama wasu 'yan uwan a kalla mutun biyar. 


na tambayi Malamin cewa ko an samu asarar rayuka?  yace zuwa yanzu basu sani ba.


 daga nan na garzaya zuwa babbar hel kwatar 'yan sanda ta Kaduna kuma nayi karo da jami'in hurda da jama'a na 'yan sandan  A S P  Mukhutar Aliyu domin ya yimin Karin haske a game da wannan hari da ake zargin sun Kai wajen muzaharar ya karamin haske da cewa, tuni dai gwamnati ta soke duk wani abu na 'yan shi'a a kaduna, kuma bayan haka gwamnati ta hana duk wata zanga zanga ko raly a kaduna, don haka bazasu bari wani ko wasu su karya wannan doka ba. 


daga karshe yace 'yan shi'ar sun raunata musu 'yan sanda biyu.


 zargin da 'yan shi'ar suka musan ta. 

kaduna

kaduna

kaduna

kaduna

kaduna

kaduna

kaduna

kaduna

kaduna

kaduna


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky