'Yan Majalisar Amruka Na Yunkurin Kiran Trump domin Ya Bada Bahasi

'Yan Majalisar Amruka Na Yunkurin Kiran Trump domin Ya Bada Bahasi

Wasu daga cikin 'yan majalisar dokokin Amurka da suka hada 'yan jam'iyyar Democrat da kuma 'yan Republican, sun fara hankoron ganin an aike wa Donald Trump da kiraye domin ya bayyana a gabansu.

Dan majalisar dattijan Amurka kuma tsohon shugaban jam'iyyar Democrat Dana Brazil ya bayyana cewa, su da wasu daga cikin 'yan majalisa na jam'iyyar Republican ta Donald Trump, suna da shirin aike masa da gayyata, domin ya zo a gaban majalisa ya amsa wasu tambayoyi.

Maxine Waters dan majalisar dokokin Amurka na ja'iyyar Democrat daga jahar California, da kuma sanata Al Green mai wakiltar jahar Texas, suna daga cikin wadanda suka shiga domin ganin an gayyaci Trump zuwa gaban majalisar dokokin Amurka, domin amsa tambayoyi biyo bayan fallasa wasu bayanan sirri da lauyansa ya yi a gaban kotu a makon da ya gabata.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Shahadar Kwamandojin Musukunci. Haj,Kasim Sulemani Da Abu Mahdi
We are All Zakzaky