'Yan Boko Haram Sun Kai Wa Sojojin Nijar Hari A Yankin Tafkin Chadi

'Yan Boko Haram Sun Kai Wa Sojojin Nijar Hari A Yankin Tafkin Chadi

Majiyoyin tsaro a Nijar na cewa, wasu mayakan boko haram sun kai hari kan sansanonin soji a kewayen tafkin Chadi.

An dai kai harin ne a cikin daren jiya Asabar wayewar wannan Lahadin, a sansanonin sojin Nijar biyu a yankin tafkin Chadi a kusa da iyaka da kasar Chadi.

Hare haren an kai su ne a sansanonin soji na Bilabrim da kuma Kulbakura, a inda bayanai ke cewa mayakan na Boko Haram sun kashe sojojin Nijar biyu, da kuma kona motocin saji uku.

Babu dai karin bayyani daga hukumomin kasar kawo yanzu.

Tun shekara 2009 ne kungiyar Boko haram ta fara kai hare harenta a Najeriya, kafin daga bisani ta fadadasu zuwa kasashen da suka hada Nijar, Kamaru da Chadi, inda ta kashe dubban mutane tare da cilasta wa wasu milyoyin kaurace wa muhallansu.Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky