Wata Kotu A Kaduna Ta Sallami Shari'ar 'Yan Shi'a

Wata Kotu A Kaduna Ta Sallami Shari'ar 'Yan Shi'a

Babbar kotun jihar Kaduna a yau Talata 31 ga Yuli, 2018 ta zartar da hukuncin da ya faranta mana wanda Lauyoyinmu suka shigar “No Case Submission ” dangane da ‘yan’uwa musulmi kusan 100 da suke tsare suna fuskantar tuhumar kisa tun bayan kisan kiyashin da aka yi mana a Zariya a Disamban 2015.

Yau dai kotu ta wanke su tare da sallamar su.

Kamar yadda aka sani cewa, yau talata(31/7/2018)ne High court 6 dake kaduna ta sanya domin yanke hukunci game da case din ‘yan,uwa da akeyi a kotun wadanda jami,an tsaro suka kama a waqi,ar zaria ta 2015.

A hukuncin na kotun, ta wanke ‘yan,uwa tace basu aikata laifi ba, ta kuma tace, a sakesu nan take ba tare da bata lokaci ba.

A yanzu haka, ‘yan,uwa dai sun wuce prison don su kwaso kayayyakinsu. Allah na tare da muminai.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky