Venezuela: An Kame Mutane 6 Bisa Zargin Yunkurin Kashe Shugaba Maduro

Venezuela: An Kame Mutane 6 Bisa Zargin Yunkurin Kashe Shugaba Maduro

Ma'akatar harkokin cikin gidan kasar Venezuela ta sanar da cafke wasu wasu mutane 6 da ake zargin cewa suna da hannu kai tsaye a yunkurin yi wa shugaba Maduro kisan gilla a jiya Lahadi.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoto daga birnin Caracas cewa, Ministan harkokin cikin gidan kasar Venezuela Nestor Reverol ya fadi a daren jiya cewa, jami'an tsaro sun samu nasarar cafke mutane 6 wadanda ake zargin cewa suna da hannu dumu-dumu a yunkurin kashe shugaba Maduro.

Ministan ya kara da cewa, a ci gaba da biciken da jami'an tsaro suke gudanarwa kan wannan lamari, sun samu wasu motoci da wasu fina-finai na bidiyo da aka dauka da suke da dangantaka da harin.

An dai yi amfani da jirgi maras matuki ne da yake dauke da wasu abubuwa masu fashewa wajen kai harin a loacin da shugaba Maduro yake gabatar da jawabi, lamarin da ya yi sanadiyyar jikkatar sojoji 7.

Gwamnatin Venezuela ta zargi gwamnatocin Amurka da Colombia da hannu wajen shirya yi wa shagaba Maduro kisan gilla, wanda bai yi nasara ba.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky