Turkiyya Ta Ja Kunnan Kasashen Da Suke Goyon Bayan Fatahullahi Gulen

 Turkiyya Ta Ja Kunnan  Kasashen Da Suke Goyon Bayan Fatahullahi Gulen

Gwamnatin Turkiyya ta yi gargadin cewa zata dauki matakin ramakon gayya kan kasashen da suke goyon bayan kungiyar Fatahullahi Gulen.

Shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyib Erdogan ya yi gargadin cewa; Duk kasashen da suka ki amsa bukatar kasarsa ta neman a mika mata 'yan kungiyar Fatahullahi Gulen, to babu makawa gwamnatin Turkiyya zata dauki matakin ramakon gayya kan kasashen.

A jawabinsa a zaman taron 'yan jam'iyyarsa ta Justice and Development Party wato AK Party a takaice; Shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyib Erdogan ya yi gargadin cewa: Rashin mika wa gwamnatin Turkiyya 'yan kungiyar Fatahullahi Gulen zai zame wata babbar hasara ga kasashen da suka dauki matakin bijirewa bukatar ta Turkiyya.

Duk da cewa Rajab Tayyib Erdogan bai ambaci sunayen kasashen da yake musu wannan barazana ba, amma a fili yake cewa: Erdogan yana nufin kasar Amurka ce da wasu kasashen yammacin Turai, kuma wannan shi ne karon farko da wani babban jami'in gwamnatin Turkiyya ya fito fili yana gargadi kan kasashen da suke goyon bayan 'yan kungiyar Fatahullahi Gulen.

Manazarta kan harkokin siyasar kasar Turkiyya suna ganin cewa: Duk da matakai daban daban da mahukuntan Turkiyya suka dauka na ganin sun shawo kan kasashen da suka bada mafaka ga 'yan kungiyar Fatahullahi Gulen ciki har da wannan gargadi mai hatsari na shugaba Rajab Tayyib Erdogan lamari ne da ke fayyace cewa: Mahukuntan Turkiyya ba zasu taba samun yadda suke so ba.

Tabbas mahukuntan Turkiyya sun gabatar da tarin dalilai da hujjoji da suka dogara da su kan zargin madugun 'yan adawar kasar Muhammad Fatahullahi Gulen da magoya bayansa da hannu a shirya makarkashiyar kifar da gwamnatin Rajab Tayyib Erdogan a watan Yulin shekara ta 2016 amma gwamnatin Amurka da na kasashen yammacin Turai ba su gamsu da tuhumce-tuhumcen da ake yi kan 'yan adawar ba, don haka suka yi kunnen uwar shegu da bukatar mahukuntan na Turkiyya, sannan kuma yana daga cikin manyan dalilan da kasashen yammacin Turai da Amurka suka dogara da shi wajen kin amsa bukatar mahukuntan Turkiyya, shirin gwamnatin kasar ta Turkiyya na gudanar da garambawul a kundin tsarin mulkin kasarta da nufin samun damar murkushe 'yan adawar Turkiyya musamman ta hanyar aiwatar da hukuncin kisa.

Bayan ga zargin Fatahullahi Gulen da magoya bayansa da gwamnatin Turkiyya ke yi da hannu a shirya gudanar da juyin mulki a kasar, a shekara ta 2013 ma gwamnatin ta Turkiyya ta zargi Fatahullahi Gulen da magoya bayansa da cewa suna kokarin tada tarzoma tare da kafa gwamnati a cikin gwamnatin kasar.

An haifi madugun 'yan adawar Turkiyya Muhammad Fatahullahi Gulen ne a aranar 27 ga watan Aprilun shekara ta 1941 a kasar Turkiyya kuma shahararre ne a fagen wa'azin addinin Islama, kuma limami, sannan kwararren marubuci kuma dan siyasa da yake da gagarumin tasiri a tsakanin al'umma, sannan yana da kungiya da ake kira da Nur Movement ko Gulen Movement, tun a watan Yunin shekara ta 1999 ya yi gudun hijira zuwa kasar Amurka, inda a halin yanzu haka yake zaune a jihar Pennsylvania ta kasar Amurka. Wasu rahotonni suna bayyana cewa: A halin yanzu haka al'ummar musulmi a sassa daban daban na duniya suna amfana da rubuce-rubucensa kan ilimin addinin Musulunci musamman a fagen harkar tattalin arziki, sannan baya ga ilimin addini yana da harkar kasuwanci mai karfi a duniya, kuma kafin tabarbarewar alakarsa da gwamnatin Erdogan, shugaban na Turkiyya ya yi ta godonsa kan ya dawo gida domin ci gaba da rayuwa amma ya ki amsa gayyatar.

Sakamakon haka masharhanta ke ganin babbar manufar gwamnatin Turkiyya ta jajurcewa kan sai an mika mata babban dan adawarta Fatahullahi Gulen ita ce; kokarin ganin ta samu damar rufe bakinsa tare da karya logonsa a harkokin siyasar cikin gidan kasarta. 288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni