Turkiya: Bamu Tsoron Duk Wata Barazana Ta Amruka

Turkiya: Bamu Tsoron Duk Wata Barazana Ta Amruka

Gwamnatin kasar Turkiya ta maida martani ga shugaban kasar Amurka Donal Trump wanda ya yi barazanar dorawa kasar takunkumi mai tsanani idan ta ci gaba da tsare wani Pasto dan kasar Amurka.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban kasar ta Turkiya yana cewa ba zai jada baya ba don barazanar takunkumi ba. Gwamnatin kasar turkiya dai tana tsare da Pasto Andrew Bruson dan jihar Carolina a kasar ta turkia tun shekara ta 2016 tare da zarginsa da aikin da tare da yan kungiyar yan ta'adda    ta PKK da kuma hannu a kokarin juyin mulkin da bai ci nasara ba a kasar ta turkiya a shekara ta 2016.

Idan an tabbatar da laifi a kansa Paston zai fuskanci dauri na shekaru 35 a gidan kaso. A halin yanzu dai an fidda shi daga gidan yari an kuma yi masa daurin talala a wani gida .


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky