Tsohon Muftin Kasar Masar Ya Gargadi Musulmi Kan Daukar Tsarin Karatun Mai Fada Da Addinin Musulunci

Tsohon Muftin Kasar Masar Ya Gargadi Musulmi Kan Daukar Tsarin Karatun Mai Fada Da Addinin Musulunci

Tsohon muftin kasar masar kuma babban malami a kasar ya yi kira ga musulmi su yi hattara da bin tsarin karantarwa na kasashen yamma wanda aka gina shi kan kiyayya ga addinin musulunci.

Kamfanin dillancin labaran RASA ya nakalto Sheikh Ali Juma'ah yana fadar haka, ya kuma kara da cewa zuwan musulmi kasashen yamma don jawo hankalin matasa da musulmi su yi hattara da tsarin karantarwa na wadan nan kasashe wanda aka gina shi bisa nuna adawa da kuma kin musulunci da musulmi

Sheikh Jumu'ah ya kara da cewa kasashen yamma sun dauka cewa ci gaba yana wajensu ne su kadai, banda haka sun dauki cewa ci gaba tana samuwa ne kadai ta hanyar 'ynci barin mutane su yi abinda suka gaba dama, ba tare da takaitasu ba. 

Malamin ya bayyana haka ne a shafinsa na facebook, ya kuma kara da cewa musulmi suna da karantarwar al-qur'ani mai girma da na manzon Allah (s), wadanda suka game kome da kome a cikin rayuwar bil'adama, idan da musulmi zasu bi umurnin Allah kamar yadda yakamata, ba'a bukatar 'yansanda da jami'an tsaro don tursasawa mutane aikata alkhairi kuma hanasu sharri. 

Daga karshe malamin ya kara da cewa a cikin yan shekarun da suka gabata, an rubuta litattafai kimani 3600 wadanda suke nuna kiyayya ga musulmi da kuma addinin musulunci a kasashen yamma.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky