Trump:A Shirye Nake Na Tattauna Da Iran

Trump:A Shirye Nake Na Tattauna Da Iran

A yayin da yake ci gaba da tsanata yin barazana da kuma bayyana kiyayarsa ga al'ummar kasar Iran, Shugaban Amurka Donal Trump ya ce a shirye yake da tattauna da hukumomin jamhoriyar musulinci ta Iran,duk lokacin da suke so, ba tare da gindaya sharadodi ba

Trump wanda ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai tare da Firaministan Italia Guiseppe Conte  a marecen jiya Litinin ya ce zai gana da shugabannin Iran muddin suna bukatar haka.

Wannan sauyin matsayi na zuwa ne kasa da mako guda bayan shugaba Trump ya gargadi shugaban Iran Hassan Rouhani cewar muddin suka cigaba da yiwa Amurka barazana za su gamu da fushin da ba su taba gani ba a tarihin duniya.

Tun kafin rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban Amurka ya soki yarjejeniyar nukiliyar da Amurka tare da kasashen duniya suka kulla da Iran, yayin da ya yi watsi da shirin bayan ya hau karagar mulki.

A makon jiya, jami’an kasar Iran sun bayyana cewar sau 8 shugaba Trump ke bukatar ganawa da shugaba Hassan Rouhani lokacin gudanar da taron Majalisar Dinkin Duniya amma shugaban na Iran na hawa kujerar naki.

Hukumomin Jamhoriyar musulinci ta Iran sun bayyana cewa tattauna da Amurka ba shi da wani amfani, ganin cewa hukumomin kasar ba su da alkawari.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky